MU TANADI KATIN ZAƁENMU DOMIN KAWO SAUYI
Amb. Aliyu Bin Abbas, Shugaban National Youth Alliance (NYA) kuma ɗan takarar kujerar Shugaban Ƙasar Nigeria a jam’iyyar Action Democratic Party (ADP), ya yi kira ga al’umma da su tashi tsaye wajen amfani da damar da suke da ita ta hanyar zaɓe domin kawo sauyi mai ma’ana a ƙasa.
A cewarsa, “Sauyin da ake buƙata a ƙasa ba zai zo da buri kaɗai ba, sai da aiki, jajircewa da kuma amfani da katin zaɓe yadda ya kamata.”
Ya bayyana cewa tanadin katin zaɓe da fitowa domin zaɓar shugabanni nagari shi ne ginshiƙin kawo sauyi a tafiyar dimokiraɗiyya, musamman ga matasa da sauran ‘yan ƙasa masu kishin ci gaban ƙasa.
Ya jaddada cewa ba za a iya cimma sauyi na gaskiya ba idan jama’a ba su yi amfani da haƙƙinsu na zaɓe ba. A cewarsa, katin zaɓe shi ne makamin da al’umma ke amfani da shi wajen yanke makomar ƙasarsu cikin adalci da fahimta.
Amb. Aliyu Bin Abbas ya kuma yi kira ga matasa da su kasance masu wayewa, bin doka da oda, da kuma shiga harkokin zaɓe cikin lumana, domin tabbatar da an samu shugabanci nagari da zai kawo ci gaba mai ɗorewa.
Ya ƙara da cewa: “Idan ba ka fita ka zaɓa ba, to ka bar wa wasu su yanke maka makomar ƙasarka.”
A ƙarshe, ya jaddada cewa Najeriya na buƙatar haɗin kai, kishin ƙasa da jajircewar al’umma domin ganin an samu sauyi na gaskiya da ake buri.
Insight Tribune News
Voice of Truth, Vision of Progress.

Comments
Post a Comment