Hon. Abdulhamid Yahaya Abba Jazzy: Matashin Jagora Mai Gina Gadar Gwamnati da Al'umma
A zamanin da ake bukatar shugabanni masu kusanci da jama'a, Abdulhamid Yahaya Abba ya fito a matsayin daya daga cikin matasan da suka sadaukar da kansu wajen hada kan gwamnati da al'umma a yankin Arewa maso Gabas.
A matsayinsa na Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan Hulɗa da Al'umma a Arewa maso Gabas (SSA Community Engagement North East), ya ci gaba da sauraron bukatun jama'a, tallafa wa matasa da mata, da kuma karfafa shirye-shiryen da ke kawo ci gaba da walwala ga al'umma.
An san Hon. Abdulhamid Yahaya Abba Jazzy da jajircewa wajen tallafawa marasa galihu, karfafa sana'o'i, da samar da damammakin rayuwa ga dubban matasa da mata a yankin Arewa maso Gabas.
A yau, mutane da dama suna kallonsa a matsayin matashi mai hangen nesa, wanda ke amfani da mukaminsa wajen kusantar jama'a, fahimtar kalubalensu, da kokarin nemo hanyoyin magance su domin tabbatar da cewa muradun al'umma sun isa ga gwamnati.
Insight Tribune News na yaba wa irin gudummawar da Hon. Abdulhamid Yahaya Abba Jazzy ke bayarwa wajen bunkasa hadin kai, ci gaban al'umma, da karfafa fata a zukatan matasa. Muna addu'ar Allah Ya kara masa hikima, lafiya, da nasara a kokarinsa na yi wa kasa da al'umma hidima.
— UMAR UMB ✍️

Comments
Post a Comment