Dr. Bala Maijama’a Wunti Ne Ya Kamata Ya Zama Tutar APC A Bauchi 2027 – Umar Umb Bauchi
Idan har da gaske masu ruwa da tsaki, makusantan Shugaban Ƙasa, da shugabannin Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi suna son jam’iyyar ta samu nasara a zaɓen 2027, to lokaci ya yi da za su saurari ra’ayin al’umma tare da bai wa mutumin da jama’a ke kira da sunansa damar zama ɗan takarar gwamna. A cewar Umar Umb Bauchi, wannan mutum shi ne Dr. Bala Maijama’a Wunti.
Umar Umb Bauchi ya bayyana cewa siyasa ba ta tsaya kan son rai ko anfani na wasu tsiraru ba, illa tana buƙatar a duba wanda yake da karɓuwa a wajen jama’a, kwarewa, nagarta, da kuma tarihin taimakon al’umma. Ya ce Dr. Bala Wunti ya nuna irin waɗannan siffofi ta hanyar ayyukan ci gaban al’umma, tallafin ilimi, lafiya da ƙarfafa matasa da mata a faɗin jihar Bauchi.
“Idan APC tana son ta ci zaɓe a Bauchi a shekarar 2027, ya kamata ta tsaya kan zaɓin da jama’a suke so. Amma idan aka fifita son zuciya ko anfani na wasu mutane wajen ɗora wanda ba zaɓin jama’a ba ne, to hakan na iya jawo asarar ƙuri’u da ɓata lokaci,” in ji Umar Umb Bauchi.
Ya ƙara da cewa al’ummar Bauchi suna buƙatar shugabanci mai hangen nesa, ƙwarewa da kishin ci gaban jama’a, kuma mutane da dama suna ganin Dr. Bala Maijama’a Wunti yana daga cikin waɗanda suka dace da wannan nauyi.
– Insight Tribune News

Comments
Post a Comment