Dr. Bala Maijama’a Wunti: Jagora Na Gari, Abin Alfaharin Jihar Bauchi


 A duk lokacin da ake magana kan shugabanci mai inganci, kwarewa, da hidima ga al’umma, sunan Dr. Bala Maijama’a Wunti na daga cikin sunayen da ke haskakawa a Jihar Bauchi da Najeriya baki ɗaya.


Dr. Bala Wunti ya gina tarihin rayuwarsa ne bisa jajircewa, ilimi, nagarta, da sadaukar da kai wajen yi wa ƙasa hidima. Tsawon shekaru da dama da ya yi a fannin man fetur da iskar gas, ya rike manyan mukamai a masana’antar makamashi ta Najeriya, inda ya bayar da gudunmawa mai tarin yawa wajen bunƙasa tattalin arziki da ci gaban ƙasa. 


Abin da ya fi daukar hankali game da Dr. Bala Wunti shi ne yadda yake haɗa kwarewar aiki da tausayi ga jama'a. Ta hanyoyi daban-daban, ya kasance mai tallafawa matasa, ilimi, kiwon lafiya, da shirye-shiryen da ke inganta rayuwar al'umma, musamman a Jihar Bauchi. 


Masana da masu sharhi kan harkokin shugabanci sun bayyana shi a matsayin mutum mai hangen nesa, wanda ya fahimci yadda ake tafiyar da manyan tsare-tsare tare da samar da sakamako mai anfani ga jama'a. Kwarewarsa a manyan cibiyoyin ƙasa da ƙasa da kuma shekaru fiye da talatin na aiki sun sanya ya zama abin koyi ga matasa masu neman nasara. 


A yau, al'ummar Bauchi da dama suna kallon Dr. Bala Maijama’a Wunti a matsayin ɗaya daga cikin fitattun 'ya'yan jihar da suka kawo wa Bauchi girma, mutunci, da alfahari a matakin ƙasa da ƙasa. Tarihinsa na gaskiya, aiki tukuru, da kishin al'umma na ci gaba da zama abin koyi ga masu tasowa. 


Insight Tribune News na yabawa irin gudunmawar da Dr. Bala Maijama’a Wunti ke bayarwa wajen gina rayuwar jama'a tare da fatan Allah Ya ƙara masa lafiya, hikima, da nasara domin ci gaba da hidimtawa al'umma da ƙasarsa.


— Insight Tribune News Desk

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS