DR. AHMAD UMAR ABDULLAHI, WAZIRIN DAMBAM YA MIƘA SAƘON TA'AZIYYA KAN RASUWAR ALHAJI SULE KATAGUM


DR. AHMAD UMAR ABDULLAHI, WAZIRIN DAMBAM YA MIƘA SAƘON TA'AZIYYA KAN RASUWAR ALHAJI SULE KATAGUM


Daga Desk na Insight Tribune


Fitaccen ɗan kasuwa, jagoran al'umma kuma Wazirin Dambam, Dr. Ahmad Umar Abdullahi, ya bayyana alhininsa da jimaminsa kan rasuwar Alhaji Sule Katagum, wanda rasuwarsa ta girgiza iyalai, abokai da al'ummar Bauchi baki ɗaya.


A cikin saƙon ta'aziyyarsa, Wazirin Dambam ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga al'umma, yana mai cewa Alhaji Sule Katagum mutum ne da ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban jama'a da kyautata zamantakewa.


"Mun karɓi labarin rasuwar Alhaji Sule Katagum cikin alhini da jimami. Wannan babban rashi ne ga iyalansa, masoyansa da al'ummar Katagum da Bauchi gaba ɗaya. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa," in ji Wazirin Dambam.


Ya kuma miƙa saƙon jaje da ta'aziyya ga iyalan marigayin, abokan arziki da daukacin waɗanda wannan rashi ya shafa, tare da addu'ar Allah Ya ba su haƙurin jure wannan babban rashi.


Wazirin Dambam ya ƙara da cewa mutuwa hanya ce da kowa zai bi, don haka ya bukaci al'umma su ci gaba da yi wa marigayin addu'a tare da ɗaukar darasi daga kyawawan halayensa da rayuwarsa.


Allah Ya jikansa da rahama, Ya haskaka masa kabari, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Amin.


Insight Tribune News.

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS