DR. AHMAD UMAR ABDULLAHI (WAZIRIN DAMBAM): JIGO A CIKIN HIDIMAR AL’UMMA DA GINA KYAKKYAWAR MAKOMA
DR. AHMAD UMAR ABDULLAHI (WAZIRIN DAMBAM): JIGO A CIKIN HIDIMAR AL’UMMA DA GINA KYAKKYAWAR MAKOMA
By Insight Tribune News
A duk lokacin da ake magana kan shugabanci nagari, tausayi ga al’umma da kuma kishin cigaban jama’a, sunan Dr. Ahmad Umar Abdullahi na daga cikin fitattun sunayen da ke zuwa a zuciyar mutane da dama.
Wazirin Dambam ya yi fice wajen nuna kishin al’umma, girmama jama’a da kuma bayar da gudummawa ga harkokin cigaba. Kyawawan halayensa, karamcinsa da yadda yake mu’amala da mutane cikin mutunci sun sa ya samu karɓuwa a zukatan jama’a daga sassa daban-daban.
Mutane da dama na kallonsa a matsayin mutum mai hangen nesa, wanda ke amfani da iliminsa da gogewarsa wajen bayar da shawarwari masu amfani da kuma tallafawa ayyukan da ke inganta rayuwar al’umma. Wannan ne ya sa yake ci gaba da samun yabo da girmamawa daga waɗanda suka san shi da kuma waɗanda suka amfana da gudummawarsa.
A yau, jama’a da dama na yi masa fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya, hikima da nasara a dukkan al’amuransa, domin ya ci gaba da zama abin koyi ga matasa da sauran al’umma.
Allah Ya ci gaba da albarkaci rayuwarsa, Ya ƙara masa ɗaukaka da nasara. Amin.
Umar Umb Bauchi ✍️
Insight Tribune News


Comments
Post a Comment