DR. ADAMU ABDULLAHI ATTERWAHMIE: GOYON BAYANSA GA GWAMNA NAMADI DANMODI ABIN A YABA NE
Daga A. A. Mu'azu Bsc, MBA, AHAN, MNIM
Tun bayan da al’ummar Jahun da Miga suka gano irin kyawawan halaye, nagarta da jajircewar Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie wajen yi wa al’umma hidima, jama’a daga sassa daban-daban suna ci gaba da tururuwa zuwa gare shi suna roƙonsa da ya shiga harkokin siyasa domin ya tsaya takara a zaɓen shekarar 2027.
Duk da cewa har yanzu Dr. Atterwahmie bai shiga siyasar jam’iyya kai tsaye ba, gudummawar da yake bayarwa wajen cigaban al’umma ta fi ta wasu da dama da suke cikin siyasa a yankin. Ya taimaka matuka wajen tallafawa matasa, bayar da guraben aiki, da kuma taimakon ɗalibai wajen samun ilimi.
A matsayinsa na ƙwararren likita a fannin kula da mata masu juna biyu da lafiyar mata, marasa lafiya da dama suna neman a duba su a hannunsa musamman a ranakun da yake gudanar da aikinsa a Asibitin FMC Birnin Kudu. Wannan na daga cikin dalilan da suka sa asibitin ya samu karɓuwa da yabo daga jama’a, musamman wajen kula da lafiyar uwa da jariri.
Gudummawar da Dr. Atterwahmie yake bayarwa ga cigaban Jihar Jigawa ta sa ya samu karɓuwa a wajen jama’a da shugabanni. Haka kuma, yana daga cikin mutanen da suka sadaukar da lokacinsu da dukiyarsu wajen wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa goyon baya ga manufofin gwamnatin Gwamna Malam Umar Namadi Danmodi.
Bayan kammala zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC, Dr. Atterwahmie ya nuna dattaku da hangen nesa ta hanyar kwantar da hankalin magoya bayansa tare da jan hankalinsu kan muhimmancin haɗin kai, haƙuri da kuma ci gaba da mara wa gwamnatin Gwamna Namadi Danmodi baya domin samun cigaba mai ɗorewa.
A yau, magoya bayansa suna ci gaba da tsayawa daram wajen goyon bayan manufofinsa na hidimtawa al’umma, haɗin kai da kuma cigaba.
Insight Tribune News

Comments
Post a Comment