DAN ADALAN MUBI MAL. MUSA JIDDA: JARUMIN ILIMI DA KYAWUN HALI DA YA ZAMA TUSHEN GIRMA GA AL’UMMA
DAN ADALAN MUBI MAL. MUSA JIDDA: JARUMIN ILIMI DA KYAWUN HALI DA YA ZAMA TUSHEN GIRMA GA AL’UMMA
Akwai wasu mutane da Allah ke ba su baiwa ta musamman wadda ba ta tsaya ga su kaɗai ba, sai dai ta zama haske ga al’umma baki ɗaya. Daga cikin irin waɗannan fitattun mutane akwai Dan Adalan Mubi, Malam Musa Jidda, wanda sunansa ya ci gaba da fitowa a matsayin ginshiƙi na ilimi, kyautatawa da nagartar zamantakewa a cikin al’umma.
Malam Musa Jidda ba mutum ne mai neman yabo ba, amma ayyukansa ne ke tilasta duniya ta yi masa shaida. Yana daga cikin mutane masu amfani da ilimi da hikima wajen gyara rayuwar jama’a, musamman wajen taimako, shawara da kuma jagoranci mai amfani ga matasa da manya baki ɗaya.
A duk inda aka ambaci gaskiya, ladabi da kuma taimakon jama’a, ana samun sunansa a sahun gaba. Wannan ne ya sa aka ci gaba da girmama shi da karramawa, domin irin tasirin da yake da shi ba na yau da kullum ba ne.
Masu kusantar shi suna bayyana shi a matsayin mutum mai zuciyar tausayi, sauƙin kai da kuma tsantsar kishin ci gaban al’umma. Duk da matsayin da yake da shi, yana ci gaba da kasancewa kusa da jama’a, yana sauraron buƙatunsu tare da ƙoƙarin kawo mafita.
Hakika, Dan Adalan Mubi Mal. Musa Jidda abin alfahari ne ga Mubi da ma Najeriya baki ɗaya. Irin wannan shugaba mai hidima ga jama’a shi ne abin da al’umma ke buƙata domin ci gaba da zaman lafiya da ci gaban ilimi.
👉 Allah Ya saka masa da alheri, Ya ƙara masa daraja, Ya kuma sa ayyukansa su ci gaba da zama haske ga al’umma.
UMAR UMB ✍️

Comments
Post a Comment