Arzikin Jihar Bauchi da Najeriya na Samun Jagora Mai Nagarta Irin Dr. Bala Maijama’a Wunti


 Jihar Bauchi da Najeriya baki ɗaya na daga cikin masu sa’ar samun ɗan ƙasa mai ilimi, tausayi, taimako da nagarta irin Dr. Bala Maijama’a Wunti. A tsawon shekaru, ya yi fice wajen hidimtawa al’umma ta fannoni daban-daban, musamman ilimi, lafiya, tallafa wa marasa galihu da kuma bunƙasa rayuwar matasa. 


Dr. Bala Wunti ya kasance abin koyi ga matasa saboda ƙwarewarsa, jajircewarsa da kuma sadaukar da kansa wajen inganta rayuwar jama'a. Ta hanyar ayyukan jin ƙai da ci gaban al’umma, ya taimaka wa dubban mutane tare da ba su damar samun ilimi, horo da tallafin rayuwa. 


Hakika, samun mutum mai hangen nesa, mutunci da son cigaban jama’a irin Dr. Bala Maijama’a Wunti wata babbar ni’ima ce ga Bauchi da Najeriya. Irin waɗannan mutane ne ke gina al’umma mai ɗorewa tare da barin kyakkyawan tarihi ga ƙarni masu zuwa. 


— UMAR UMB ✍️

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS