AL'UMMAR SOKOTO EAST ZA SU ZAƁI AJIYAN SOKOTO A 2027 – UMAR UMB


 

Alhaji Umar Ajiya Isa (Ajiyan Sokoto) na ci gaba da samun karɓuwa da goyon baya daga al'ummar Sokoto East sakamakon nagarta, jajircewa da kuma gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban jama'a.


A cewar Umar Umb, al'ummar Sokoto East suna buƙatar shugaba mai hangen nesa, gaskiya da kishin talakawa, kuma Ajiyan Sokoto ya cika waɗannan siffofi. Ya bayyana cewa shekarar 2027 za ta kasance dama ga al'umma su zaɓi wakili nagari wanda zai kare muradunsu tare da kawo ci gaba mai ɗorewa ga mazabar.


"Mun yi imani cewa Alhaji Umar Ajiya Isa (Ajiyan Sokoto) shi ne zaɓin da ya dace domin wakiltar Sokoto East a Majalisar Dattawa. Tarihinsa na taimakon jama'a da kishin ci gaban yankinsa sun sanya mutane da dama ke kallonsa a matsayin mafita ga ci gaban mazabar," in ji Umar Umb.


Allah Ya ba al'ummar Sokoto East mafificin zaɓi a shekarar 2027.


Insight Tribune News

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS