AJIYAN SOKOTO YA ƘADDAMAR DA COORDINATOCIN YAƘIN NEMAN ZAƁENSA A SAKKWATO TA GABAS

 


AJIYAN SOKOTO YA ƘADDAMAR DA COORDINATOCIN YAƘIN NEMAN ZAƁENSA A SAKKWATO TA GABAS


Daga Insight Tribune News


Ɗan takarar kujerar Sanatan Sakkwato ta Gabas a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Hon. Alhaji Umaru Ajiya Isa (Ajiyan Sokoto), ya ƙaddamar da coordinatocin yaƙin neman zaɓensa daga ƙananan hukumomi takwas na shiyyar Sakkwato ta Gabas a yau Juma’a, 19 ga Yuni, 2026.


An gudanar da taron ƙaddamarwar ne a Sakatariyar Haɗin Gwiwar Yaƙin Neman Zaɓen Sanata ta Ajiyan Sokoto da ke kan Titin Kontagora a Birnin Sakkwato, inda manyan shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki, jiga-jigan APC da ɗimbin magoya baya daga sassa daban-daban na yankin suka halarta.


Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Maigirma Kwamandan Yaƙin Jam’iyyar APC a Gabascin Sakkwato kuma Zonal Vice Chairman, Alhaji Muhammadu Musa Sarkin Alaru Illela, tare da haɗin gwiwar kwamitin tsarawa da shirya harkokin tafiyar siyasar Hon. Umaru Ajiya Isa a gida da wajen jihar.


A jawabinsa, Ajiyan Sokoto ya bayyana matuƙar godiyarsa ga al’ummar Sakkwato ta Gabas bisa irin goyon baya, amincewa da ƙaunar da suke ci gaba da nuna masa. Ya kuma jaddada muhimmancin aiki da gaskiya, riƙon amana da kishin al’umma ga coordinatocin da aka ƙaddamar, domin tabbatar da isar da manufofi da saƙonnin tafiyarsa ga mazaɓu a kowane mataki.


Masu sa ido kan harkokin siyasa na kallon wannan ƙaddamarwa a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa tsarin yaƙin neman zaɓen Ajiyan Sokoto, tare da nuna yadda tafiyarsa ke ci gaba da samun karɓuwa da goyon baya a faɗin shiyyar Sakkwato ta Gabas gabanin babban zaɓen da ke tafe.


Umar Umb ✍️

Insight Tribune News

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS